Rahotanni daga Jihar Katsina sun tabbatar da cewa, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki kauyen Daddara da ke Karamar hukumar Jibiya, inda suka kashe mutum shida, cikinsu har da Dagacin garin.
Maharan sun kuma sace karin wasu mutum biyar, kamar yadda wani daga cikin mazauna kauyen na Daddara ya tabbatar wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a sanyin safiyar ranar Alhamis.
Mutumin, wanda ’yarsa na cikin wadanda maharan suka yi garkuwa da su, ya ce, ’yan bindigar sun kashe Dagacin garin, Alhaji Jafaru Rabi’u, wanda aka fi sani da Magaji Yangayya da kuma yaron gidansa, Malam Nasir Danye.
“Sun kashe Dagaci da hadiminsa da kuma wasu mutane, sannan sun sace ’ya ta da ke aure a garin. A nan babban garin Daddara kuma sun kashe mutum hudu, sannan suka sace wasu, kuma wasu sun jikkata yayin tsira da ransu,’yan bindigar sun shiga cikin gida-gida inda suka saci dabobbi, kayan abinci da kuma kudade daga hannun mutanen da suka shiga gidajensu”. A cewar mutumin.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wata sanarwa daga rundunar ’yan sandan Jihar ta Katsina, sakamakon, SP Gambo Isah bai daga waya ko amsa rubutaccen sakon kar-ta-kwanan da Aminiya.