Ƴan bindiga sun afkawa kauyen Kukar Babangida da ke karamar hukumar Jibia na jihar Katsina, inda suka kashe dagacin kauyen Magaji Haruna da ɗansa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kuma kashe wasu mutum takwas a harin da aka kai da misalin karfe 10 na dare ranar Laraba.
Har ila yau, wani mazaunin garin ya bayyana cewa an tafi da mata wanda ba a san adadinsu ba zuwa yanzu.
Mazauna garin sun yi imanin cewa akwai manyan shugabannin ƴan bindiga biyu da ke cin karensu babu babbaka a ciki da wajen karamar hukumar ta Jibia.
Ƙauyen Kukar Babangida ya kasance ɗaya daga cikin kauyuka da ke fama da matsalar ƴan bindiga tun bayyanar ayyukansu a faɗin jihar.