fidelitybank

‘Yan bindiga sun kashe babban Limamin juma’a a Zamfara

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari jihar Zamfara, inda suka kashe Sheikh Ahmad Rufa’i, babban limamin babban masallacin Juma’a na kauyen Keita a karamar hukumar Tsafe a jihar.

Harin ya faru ne jim kadan bayan musulmi sun yi sallar isha’i (dare) a jam’i.

Wannan mummunan lamari dai ya zo ne makonni uku kacal bayan kisan da aka yi wa Imam Abubakar Hassan Mada babban limamin babban masallacin garin Mada, karamar hukumar Gusau.

A cewar Ibrahim Musa Keita, wani mazaunin kauyen Keita, an fara ganin barayin ne a kan hanyar Kwarin Gano zuwa Keita.

Duk da an sanar da mazauna garin, ‘yan fashin sun ci gaba da mamaye kauyen.

Bayan sun kasa sace masu amfani da hanyar, sun kai hari kauyen Keita, inda suka kashe babban limamin, tare da yin awon gaba da mutane da dama ciki har da mata.

“Kafin mamayar, an sanar da mazauna garin game da motsin ‘yan bindigar a kan titin Kwarin Gano-Keita.

“An hango su a kan hanyar amma ba mu da tabbacin ko za su zo wannan kauyen ko a’a.

“Da farko sun so su yi awon gaba da masu amfani da hanyar a kan hanyar Keita zuwa Kwarin Gano, amma bayan sun dauki lokaci ba tare da samun ko mutum daya ba, sai suka mamaye kauyen Keita, suka kashe babban limamin mu tare da sace mutane da dama ciki har da mata.

“Ba mu tantance adadin mutanen da suka yi garkuwa da su ba yayin da wasu suka ruga cikin daji har yanzu ba a gansu ba.” Ya bayyana.

A wani labarin kuma, an yi garkuwa da wasu mutane biyu a kauyen Magazu dake karamar hukumar Tsafe da sanyin safiyar Talata.

‘Yan bindigar a cewar wani mazaunin kauyen Yusuf Ibrahim, sun mamaye kauyen ne da misalin karfe uku na safe, inda suka rika harbe-harbe.

Ibrahim ya kara da cewa yawancin mazauna garin sun bar gidajensu.

Wani mazaunin kauyen Kwalfada, Aminu Kwalfada, ya koka kan yadda fargabar ‘yan bindiga ke sa jama’a daina amfani da lasifika a masallatai a lokutan sallah.

ASP. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Abubakar Yazid, bai iya bayar da cikakken bayani ba har zuwa lokacin da aka bayar da rahoton, amma ya yi alkawarin bayar da bayanai da zarar an samu.

national tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp