Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba a ranar Asabar ,sun kai hari kauyen Gambar Sabon Layi da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi.
Rahotanni daga yankin na cewa ‘yan bindigar da har yanzu ba a tantance ko su wanene ba sun kashe mutane biyar tare da yin garkuwa da mutum daya a cikin lamarin lamarin da ya jefa al’umma cikin rudani.
Wani mazaunin unguwa ya shaida cewa ‘yan bindigar sun zo ne cikin dare inda suka rika harbin iska don tsorata mazauna yankin kafin su aiwatar da wannan mugunyar aikin nasu.
Ya ce sun yi garkuwa da Mista Danie, sannan suka kashe hakimin unguwar yayin da aka kashe wasu hudu.
Wani mazaunin yankin, Mista Manasseh Danladi ya ce: “A jiya (Asabar), wasu mutane sun zo kauyenmu suka kashe kawuna tare da wasu hudu yayin da aka tafi da Mista Daniel.” In ji Tribune.