‘Yan bindiga sun yi wa tawagar jami’an tsaron ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP Ifeanyi Okowa kwanton ɓauna tare da kashe ‘yan sanda uku.
Rahotonni sun ce maharan sun far wa tawagar jami’an tsaron lafiar gwamnan, da suka hada da ‘yan sanda huɗu a daidai garin Ihiala da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Wasu majiyoyi sun ce jami’an tsaron na kan hanyarsu ta zuwa jihar Abia, inda tsara mista Okowa zai je domin ganawa da wasu mambobin jam’iyyar PDP a jihar gabanin babban zaɓen ƙasa da ke tafe ranar 25 ga watan da muke ciki.
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da faruwar lamarin.
A jerin wasu saƙonni da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar Ifeanyi Okowa ya miƙa sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar da iyalansa zuwa ga iyalan mamatan, waɗanda ya bayyana a matsayin ‘jajirtattu’.
Tare da yin addu’ar samun rahama a gare su, sannan kuma yi alƙawarin nema wa iylansu haƙƙinsu.
Harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan tawagar daraktan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP na jihar Rivers a birnin fatakwal.