fidelitybank

‘Yan bindiga sun kai hari Coci sun sace mutane 9 a Katsina

Date:

‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun sace masu bauta tara a wani coci a ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina.

Rahotonni sun ce ‘yan bindigar sun je cocin ne da ke unguwar Gidan Haruna a kan babura da safiyar ranar Lahadi a lokacin da masu bautar ke gudanar da addu’o’insu.

Reveran Yusuf Haruna shugaban ƙungiyar CAN reshen ƙaramar hukumar Kankara ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun sace mutum tara ciki har da mata bakwai da yara biyu.

Ya ƙara da cewa maharan sun daki wani magidanci tare da karya shi a lokacin da suka kai harin.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin arewacin ƙasar da ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka.

A watan Disamban 2020 ‘yan bindiga sun kai wani hari makarantar sakandiren Kankara tare da yin garkuwa da ɗalibai 300, waɗanda daga baya a ka sako su.

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp