Hankula jama’a sun tashi yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, suka bindige ‘yan sanda uku har lahira a shingensu a jihar Enugu.
Lamarin ya faru ne a kan mahadar Timber junction, kusa da Maryland a karamar hukumar Enugu ta Kudu.
Vanguard ta gano cewa, wani direban Keke Napep ya jikkata sakamakon harsashin da miyagun suke ta harbawa, domin su firgita mutane.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Enugu ya tabbatar da afkuwar lamarin, duk da bai bada cikakken bayani ba.