Wasu ‘yan bindiga sun harbe babbar matar babban limamin masallacin makiyaya da ke Rugan Ardo, Isyaka Adamu, har lahira.
Misis Hulaira Hussaini Ardo, an harbe ta ne bayan ‘yan fashin sun karbi Naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa.
Tun a ranar 11 ga Fabrairu, 2023, ‘yan bindiga sun sace matan Malam Husaaini Ardo hudu a Rugan Ardo a karamar hukumar Kagarko, suka kashe babban limamin masallacin makiyaya da ke Rugan Ardo, Isyaka Adamu.
Madaki na Janjala, Samaila Babangida, ya tabbatar da kisan, kuma ya ce al’ummar garin na cikin alhinin kashe matar sarkinsu, inda ya ce barayin sun ki sakin gawar ta.
A cewarsa, an biya kudin fansa naira miliyan 2 domin sakin matan hudu, amma ‘yan fashin sun harbe babbar matar, yayin da sauran ukun suka sako.
Ya ce bayan an kai kudin fansa ga ‘yan fashin tare da ba da tabbacin ‘yantar da matan sarki hudu ne shugaban ‘yan bindigar ya harbe babbar matar tare da sakin sauran ukun.
“Na hau daya daga cikin baburan da ya kai musu kudi da kayan abinci. Bayan sun karbi kudin ne shugabansu ya bude wa babbar matar wuta,” inji shi.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige bai amsa kiran da aka yi masa ba da kuma sakon da aka aike masa