Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ,ya rasa daya daga cikin hadiman sa.
Wasu ‘yan bindiga sun harbe Cyril Mudiagbe a garin Sapele da ke karamar hukumar Sapele a jihar Delta.
Wanda aka fi sani da Cyril Makanaki, dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne da ke Ward 6 a Sapele.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi a gidansa da ke unguwar Decima.
Wani makwabci mai suna Eniagbe ya ce ‘yan bindigar sun harbe marigayin ta tagar.
“Suna buga tagar sa kuma lokacin da ya bude tagar, an harbe shi a kirji”, in ji shi.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun fara farautar maharan.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda,a Delta, Bright Edafe ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.