Bayan shafe kwanaki hudu da yi wa mutane kisan gillan da aka yi wa mutane 12 a Daraga a jihar Zamfara, har yanzu ba a iya yi masu jana’iza ba a yankin.
‘Yan bindigan da suka yi ta’adin sun ki ficewa daga kauyen, domin haka an gagara birne gawawwakin mutanen da a ka kashe.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa, duk sun tsere sun bar gidajensu a karkarar.
Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, inda aka ji al’ummar kauyen Daraga a karamar hukumar Maru su na kokawa a game da halin rashin tsaron da suke ciki. Mutanen da ke zama a yankin sun shaidawa BBC Hausa cewa sun gagara binne ‘yanuwansu da aka hallaka, saboda har yanzu ‘yan bindiga sun ki barin garinsu.
Wani mutumi da ya zanta da manema labarai ba tare da ya bari an kama sunansa ba, ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun kona gidansa, sun bindige mutanensa. Baya ga ‘danuwansa da aka kashe, wannan mutum ya ce, ‘yan bindigan sun harbe ubangidansa a shago.