‘Yan bindigan da suka yi garkuwa da mutane sama da 30 a baya-bayan nan a karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara, mahaifar karamin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle, ya bukaci a biya Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa.
Wani mazaunin yankin mai suna Ibrahim Maradun ya shaidawa manema labarai, cewa duk wata hanya da ake da ita don tara kudin ta zama tabarbare saboda masu hannu da shuni ba su nuna damuwar biyan kudin fansa ba.
“Muna da attajirai a garin amma ba za su iya yin kasada da dukiyoyinsu ba domin wadanda aka sace su kwato ‘yancinsu daga ‘yan bindigar,” in ji shi.
Maradun ya bayyana cewa tun da lamarin ya faru, gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ba su bayar da wata sanarwa a hukumance ba.
“Gwamnatin jihar ba ta ziyarci garin don nuna juyayi ba, haka kuma Gwamnan bai wakilta wani jami’in gwamnati don nuna damuwa ba,” in ji shi.
Maradun ya lura cewa al’ummar yankin sun yi wa tsohon Gwamna Matawalle tawaye ta hanyar akwatin zabe saboda rashin tsaro.
“A yayin yakin neman zabe, Gwamna Dauda Lawal ya tabbatar wa da masu zabe cewa idan aka zabe shi a kan mulki, zai kawo karshen ayyukan ‘yan fashi a cikin kwanaki 100 na mulki.
“Amma yanzu, lamarin yana kara ta’azzara yayin da ayyukan ‘yan bindiga ke ci gaba da ta’azzara ba tare da la’akari da hakan ba.
“Kwanan nan, ‘yan bindiga sun yi wa jami’an tsaron jihar kwanton bauna, da aka fi sani da Community Protection Guard, CPG, sun kashe uku daga cikinsu, suka raunata da dama tare da kwace musu makamai,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an sako mutanen da aka sace.