Wani bala’i ya afkawa al’ummar kabilar Buh dake yankin Nakere a karamar hukumar Wamba a jihar Nasarawa yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a yankin.
Harin ya yi sanadin mutuwar wani shugaban matasa, Tari Moses Gbaja, wanda aka fi sani da T Boy.
Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu da misalin karfe 9 na dare, an kuma yi garkuwa da wani dan kasuwa, Nnamani Albert, da Tabitha Dauda Musa, matar shugaban limamin cocin Christ-Elect Revival Mission.
‘Yan bindigar sun raunata wasu mazauna yankin.
Kokarin samun tsokaci daga ‘yan sanda game da lamarin ya ci tura har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.