Rahotanni na nuni da cewa, ‘yan bindiga sun banka wuta a makarantar sakandaren gwamnati ta Allawa a karamar hukumar Shiroro a jihar Neja cikin tsakiyar daren Alhamis.
Har yanzu dai ba samu bayanai dangane da ainihin wadanda lamarin ya shafa ba, kasancewar yadda jami’an tsaro suka mayar da makarantar sansanin su.
Wani jigon matasan Shiroro, Sani Abubakar Yusuf Kokki ya sanar da manema labarai yadda ‘yan ta’addan suka afka sansanin sojin daga bisani kuma suka kai wa jami’an tsaron hadin guiwa farmaki.
The Nation ta rawaito cewa, duk da dai ba a gano asalin yawan wadanda lamarin ya shafa ba har lokacin rubuta wannan rahoton, amma an bayanai sun nuna a kan yadda suka kai farmakin makarantar wacce ta kasance sansanin jami’an tsaro.