fidelitybank

‘Yan bindiga sun afka Cocin Ogun yayin da suka kashe Fasto

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun afka Cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ da ke jihar ogu, lokacin da ake tsaka da ibada, inda suka kashe Fasto tare da yin garkuwa da masu ibada bakwai.

Jaridun ƙasar sun ambato kwamandan rundunar tsaron sa kai ta ‘So-Safe Corps’ Soji Ganzallo ne ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Lahadi da safe.

Ya ce dakarunsa sun samu nasarar kuɓutar da mutum bakwai tare da kashe mutum guda daga cikin maharan.

Cikin wata sanarwa da rundunar tsaron ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalain ƙarfe 12 na rana.

Inda suka afka wa Coci tare da yin garkuwa da mutum bakwai bayan sun kashe Faston.

Sanarwar ta ce an umarci jami’an tsaron sa kan na ‘So-Safe Corps’ da su kuɓutar da mutanen ba tare da raunata su ba, daga nan ne kuma jami’an suka bi sawunsu, inda suka samu nasarar kubutar da mutanen tare da kashe ɗan bindiga guda.

Mista Ganzallo ya ce jami’an rundunarsa tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun ƙaddamar da farautar sauran maharan da suka tsere domin kamo su.

yola news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp