Rundunar sojojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta ke cewa wasu ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare a shiyar Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya na amfani da wasu hanyoyin yaudara da za su iya kai ga tayar da rikici a ƙasa.
Bayanin ya ƙara da cewa akwai hujjojin da ke nuna cewa ‘yan ta’addan na amfani da dabarun dasa nakiya da sauran abubuwa masu fashewa wajen kai hare-hare, abinda zai jefa tsoro cikin zuƙatan mutane.
Sai dai rundunar sojojin ta ce a shirye ta ke domin bankaɗo duk wani makirci da ‘yan ta’addan ke amfani da shi ko da kuwa ya kasance mai tsanani.
Babban hanfsan sojojin Najeriya Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja ne ya sanar da hakan a ranar Jumu’a a helkwatar Sojoji da ke Abuja, lokacin da ya ke karɓar baƙuncin mai taimakawa Babban Sakataren Majalisar Ɗunkin kan sha’anin yaƙi da ayyukan ta’addanci, Vladimir Voronkov.
Babban hafsan sojojin ya kuma ce a shirye rudunar ta ke don yin haɗin gwiwa da Majalisar Ɗunkin Duniyar don ganin an maido da zaman lafiya a yankunan ƙasar.
Ya ce za su yi amfani da kowane mataki da ya dace domin tabbatar da nasarar hakan.
Ya kuma nemi tallafin Majalisar Ɗunkin Duniyar da sauran hukumomi masu zaman kansu domin ɗaukar matakin da ya fi dacewa ga tubabbun ‘yan ta’adda.
Mai taimakawa Babban Sakataren Majalisar Ɗunkin Duniya, Vladimir Voronkov, ya sha alawashin cewa hukumarsa za ta tallafawa Najeriya wajen gano da kuma gurfanar da masu aikata muggan laifuka.


