Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, ta musanta zargin kashe wasu mutane goma da wasu mahara suka yi a karamar hukumar Alkaleri inda aka gano mai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ahmad Wakil, ya ce labarin karya ne da nufin kawo rudani.
A cewar sa, “Rahoton na iya kawo cikas ga kokarin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na dakile miyagun laifuka a jihar.”
Ya yi bayanin cewa rundunar ‘yan sandan ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da rashin tsaro, musamman a kewayen Alkaleri, inda ya kara da cewa an samu zaman lafiya a yankin.
Ya bayyana cewa, a ci gaba da kaddamar da filin mai na Kolmani, rundunar ta tura karin kadarori da kuma kara kaimi wajen tattara bayanan sirri, da kuma aikin sintiri don lalata ayyukan da ba na gwamnati ba a yankin.
Rundunar ‘yan sandan ta jaddada bukatar kungiyoyin yada labarai su rika tantancewa a kodayaushe tare da tabbatar da cewa rahotannin sun fito ne daga majiyoyi masu inganci don samun rahotanni na gaskiya.