fidelitybank

‘Yan adawa ba za ku gane karfin APC ba sai ranar zabe – Badaru

Date:

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce, jam’iyyun adawa za su fahimci banbancin jam’iyyar da jama’a suka zaba da kuma wadanda ake raina a zaben 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake jawabi ga dimbin jama’a a karamar hukumar Kaugama. Ya kuma mayar da martani ne kan lalata fastoci da allunan talla na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ake zargin jam’iyyun adawa sun yi.

Ya ce jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta samar da fili mai kyau ga daukacin jam’iyyun adawa na jihar.

A cewarsa: “Abin takaici ne matuka, a matsayinmu na jam’iyyar da ke mulki, ba mu ci zarafin kowa ba, ba mu lalata fosta da allunan wata jam’iyya ba, har yanzu wasu jam’iyyun adawa suna lalata namu.

“Jam’iyya mai karfi ba za ta shiga cikin wani fada ko lalata dukiyoyin ‘yan adawa ba amma kawai tana nuna bambance-bambance a ranar zabe.”

Badaru, ya kuma kara da cewa jam’iyyun adawa za su fahimci bambancin da ke tsakanin jam’iyyar da ta zabi jama’a da kuma wadanda aka raina.

Barnata allunan tallan na APC, ya bayyana cewa, ba zai shafi farin jinin jam’iyyar ba, illa kara yawan magoya bayanta.

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp