Duk da ƴakin da ke yi amma wasu wasu masoya ƴan ƙasar Ukraine sun yi bikin aure irin na sojoji da aka gudanar a shingen bincike kusa da birnin Kyiv da ke fuskantar barazanar sojojin Rasha.
Magajin garin Kyiv – kuma tsohon zakaran damben boksin ajin masu nauyi na duniya – Vitaliy Klitschko, yana cikin waɗanda suka shaida auren.
Valery da Lysia, waɗanda suka shiga yaƙin Ukraine a matsayin ƴan sa-kai sun yanke shawarar bikin aurensu a fagen daga domin aurensu ya kasance wani labarin da za a tuna wata rana.