Wani ɗalibi ɗan asalin Zambia wanda ke karatu a Rasha, ya rasa ransa a fagen yaƙi a Ukraine, a wani yanayi mai ɗaure kai.
Ministan tsaro na Zambia ya shaida wa manema labaru a Lusaka cewa, dama dai ɗalibin yana zaman kaso ne a ƙasar ta Rasha.
Ɗalibin mai suna Lemekhani, mai shekara 23, yana karantar ilimin nukiliya ne a Moscow Engineering Physics Institute, amma a shekarar 2020 an yanke masa ɗaurin shekara tara bayan samun sa da wani laifi da ba a fayyace ba.
Ministan harkokin wajen na Zambia, Stanley Kakubo, ya faɗa wa manema labarai a yau Litinin cewa, Nyirenda, wanda ɗaya ne daga cikin ɗaliban da gwamnati ke ɗaukar nauyin karatunsu a ƙasar ta Rasha, an kashe shi ne tun cikin watan Satumba, amma sai yanzu ne hukumomin Rasha suka sanar da ƙasar ta Zambia.
Ya ce saboda haka “gwamnatin Zambia ta buƙaci Rasha ta yi mata bayani dalla-dalla kan yadda aka yi ɗalibin da ke zaman kaso ya samu kansa cikin aikin soji kuma aka tura shi yaƙi a Ukraine, inda ya rasa ransa.”
Ya ce yanzu haka ana shirye-shiryen mayar da gawar ɗalibin gida daga Rasha.
Ya ƙara da cewa “ina tattaunawa da iyalan mamacin, kuma zan ci gaba da tattaunawa da su domin bayyana masu duk bayanin da muka samu game da mutuwar ɗan’uwan nasu.”
Ba a dai san yadda aka yi Nyirenda ya fito daga gidan yari ba, amma Rasha ta rinƙa yi wa fursunoni tayin sakin su idan suka amince za su fafata a faɗan da take yi da Ukraine.