Gwamnatin Najeriya ta shawarci ‘yan ƙasar da yaƙi ya ritsa da su a Ukraine da su tsallaka zuwa ƙasar Poland mai maƙotaka, domin samun taimako.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar, ta shawarci ‘yan Najeriya su shiga Poland ta kan iyakoki huɗu tsakaninta da Ukraine.
“Ma’aikatan jakadancin Najeriya da masu aikin sa-kai na nan suna jira da motoci, domin kwashe ‘yan Najeriya a kan iyaka,” a cewar sanarwar mai ɗauke da adireshin da ta ce ‘yan Najeriya su nuna wa jami’an kan iyaka idan sun ƙarasa.
Tun ranar Alhamis Najeriya ta ce, za ta shirya aikin ceto na musamman, amma daga baya ta ce, ba za ta iya ba har sai an buɗe filayen jiragen sama na Ukraine.
A yau Asabar Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya gana da jakadun Ukraine da Rasha a Abuja babban birnin ƙasar.