Gwamnatin tarayya ta umurci karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da sauran hafsoshin soji da su koma jihar Sokoto domin kawar da yankin Arewa maso Yamma daga barazanar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Gwamnatin ta ce wannan umarnin wani bangare ne na kara kaimi wajen kawar da yankin Arewa maso Yamma daga matsalolin ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma ta’addanci.
Gwamnatin tarayya ta bayyana bakin cikinta dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a jahohi da kewaye, inda ta bayyana cewa wannan dabarar da ta dauka ya nuna jajircewar gwamnati na maido da zaman lafiya da tsaro a yankin.
A cewar sanarwar, yayin da suke yankin Arewa maso Yamma, za su sa ido kan yadda ake gudanar da ayyuka tare da tabbatar da cewa an fatattaki Bello Turji da ‘yan bindigar sa.
“Wadannan ’yan fashin sun rika yada bidiyon wata mota kirar sulke ta sojojin Najeriya da ta makale a wani wuri mai cike da ruwa.
“Kuma da daddare aka bukaci jami’an da su janye don gudun kada ‘yan bindiga su yi musu kwanton bauna, daga baya cikin dare ‘yan fashin suka je wurin, inda suka dauki hoton motar sulke da ta makale suna murna.
“Wannan lamari ya faru ne a kwashabawa, karamar hukumar Zurmi a Zamfara.
“Wannan ba abu ne da za a amince da shi ba, kasancewar shugaban kasa Bola Tinubu yana bayar da gagarumin goyon baya ga rundunar sojojin Nijeriya.
“Gwamnatin tarayya ta damu matuka game da barazanar ‘yan bindiga da ta’addanci a yankin Arewa maso Yamma.
“Saboda haka a shirye muke mu tura dukkan kadarorin da suka wajaba don tabbatar da cewa an kawar da wadannan masu aikata laifuka tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’ummominmu,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ce akwai bukatar a gaggauta daukar matakin yakar ‘yan ta’addar domin baiwa jama’a damar tafiya cikin walwala.
Sannan kuma ta tabbatar wa al’ummar jihohin Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kebbi da ma daukacin yankin Arewa maso Yamma cewa jami’an tsaro ba za su bari a fatattaki ‘yan bindigar ba.