Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce rikicin siyasar da ke faruwa a jihar Ribas bai dauke hankalinsa ban a kin aiwatar da ayyukansa na birnin tarayya.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a lokacin da yake duba wasu muhimman ayyuka da shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar a ranar 27 ga watan Mayu domin cika shekara daya kan karagar mulkinsa.
Ya ce, rikicin ya dauke hankalinsa wanda a baya hankalinsa ya karkata a kai, amma duk da haka bai hana shi aiwatar da ayyyuka da dama baa birnin tarayya.
Rahotanni na cewa, da dama Wike ya mayar da hankalinsa a kan rikicinsa tsakaninsa da shi da magajinsa Siminilaye Fubara.
Sai dai tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyensom Wike, ya ce, Tinubu zai kaddamar da ayyukansa nan da kwanaki tara kacal.