fidelitybank

Yajin aikin ASUU: An ta shi babu dadi tsakanin ministan ilimi da shugabannin dalibai

Date:

An tashi baran-baran a tattaunawa tsakanin ministan ilimi Adamu Adamu da shugabannin ɗalibai a Najeriya kan batun yajin aikin ƙungiyar malaman jami’a ta ASUU a Abuja.

Ɗaliban sun zargi ministan ilimi da ficewa zauren tattaunawar bayan sun gabatar da ƙorafinsu.

A lokacin da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ɗaliban na Najeriya Sunday Ashefon ya faɗa wa ministan cewa ya kai ɗansa ƙasar waje karatu.

Bidiyo ya nuna yadda shugaban yake jawabi da kuma yadda ministan ya bayar da amsa da ficewa daga zauren tattaunawar.

“Mun gani a kafofin sada zumunta, kana biki ɗanka ya kammala karatu a ƙasar waje.yayenmu ba su da kudin kai mu ƙasahen waje, muna son a ware kuɗi domin ci gaban ilimi a ƙasar nan, mai girma minista muna son mu koma makaranta,” kamar yadda shugaban ɗaliban ya shaida wa Adamu Adamu.

Ministan ya ce, “abu ɗaya” da ya karba a tattaunawar shi ne batun shigar ɗalibai a tattaunawa da malaman jami’a, daga nan ya fice ya bar ɗaliban a wurin tattaunawar.

Yajin aikin na gargadi da malaman jami’a suka shiga suna neman gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a 2009 kan ƙarin kuɗaɗen da ake kashewa ɓangaren ilimi.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp