Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta soke jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Qualifying, sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago suka yi.
Ma’aikatar ta sanya ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023, don gudanar da jarrabawar amma yanzu ta dakatar da shi har abada.
Sanarwar ta kara da cewa, “Ma’aikatar Ilimi ta Jiha, ta dakatar da jarrabawar shiga makarantun sakandire (SSQE) na shekarar 2023 da aka shirya gudanarwa a yau Talata 14 ga Nuwamba, 2023 har sai an sanar da ita.”
Sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar, Balarabe Abdullahi Kiru, ta yi kira ga dalibai da iyaye/masu kulawa da su jure duk wata matsala da dakatarwar ta haifar.