fidelitybank

Yajin aiki wahala zai ƙarawa ƴan ƙasa kawai – Labour Party

Date:

Jam’iyyar Labour ta yi kira ga ƙungiyoyin ƴan ƙwadago  da su sake tattaunawa da gwamnati a kan maganar sabon albashi mafi ƙanƙanta maimakon shiga yajin aiki.

Jam’iyyar ta ce a halin da Najeriya take ciki yajin aiki ba shi da amfani hasali ma zai iya ƙara wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke ciki ne.

Babban sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Obiora Ifoh ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

Ya ce tuni daman ƴan Najeriya na fama da katutun matsaloli, a don haka babu buƙatar yin abin da zai ƙara waɗannan wahalhalu.

” Ina ganin neman Naira 494 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ba abu ne mai yuwuwa ba. Abu ne da ba zai ɗore ba saboda hakan na nufin cewa Najeriya za ta ɗauki duk kuɗin da take da shi ta riƙa biyan ma’aikata,” in ji shi.

Mista Ifoh ya ƙara da cewa kamata ya yi shugabannin ƙwadagon su ci gaba da tattaunawa da gwamnati a samu matsaya kan abin da zai zama karɓabbe ga ɓangarorin biyu.

Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon na Najeriya na neman gwamnati ta tsayar da Naira 494,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma’aikatan gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba, yayin da gwamnati ke cewa Naira 60,000 za ta amince, abin da ƴan ƙwadagon suka yi watsi da shi.

Rashin cimma matsaya a kan batun a tattaunawar kwamitin musamman na albashin da wakilan ƙungiyoyin ƙwadagon, ranar 28 ga watan da ya wuce, Mayu ya sa ƙungiyoyin tsunduma yajin aikin daga yau Litinin.

vgn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp