Gwamnatin tarayya ta ce, za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a mako mai zuwa, domin kawo karshen yakin aiki.
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi Chris Ngige ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wajen wani taro da wakilan gwamnati da kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT) suka gudanar a Abuja.
Sanata Ngige ya yi nuni da cewa, da a ce za a iya kawar da rikice-rikicen masana’antu da dama a fannin ilimi, da a ce kungiyoyin sun yi amfani da manufofinsa na bude kofa, kamar kungiyoyin kiwon lafiya, wanda ya ce, ya kai ga warware matsalolin da ke addabar ma’aikata a fannin lafiya.
A wata sanarwa da mukaddashin kakakin yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi ta tarayya Patience Onuobia ta fitar, ministar wadda ita ma ta yi fatali da adawar da ke tsakanin kungiyoyin ilimi, ta bayyana cewa, kowa na da muhimmanci a tsarin jami’o’in.