Ƴan’uwan Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su a Gaza sun bayyana fushinsu kan rahotannin da ke cewa Firaiminista Benjamin Netanyahu na son sojoji su mamaye gaba ɗaya yankin har da wuraren da waɗanda ke tsaren suke.
Hukumar Falasɗinawa ita ma ta yi tur da rahoton wanda zuwa yanzu ba a tabbatar da shi ba.
Rahotannin da aka samu zuwa safiyar yau Talata sun nuna cewa aƙalla Falasɗinawa 12 aka kashe a sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai har da mutum uku da suka jiran abinci kusa da Rafah a kudancin zirin.
A jiya Litinin, rahotanni sun bayyana kisan mutane da dama.