Jakadan Falasdinawa a Najeriya, ya yi ikirarin cewa hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a kan Zirin Gaza tun bayan harin da Hamas ta kai wa kasar, sun yi sanadin mutuwar kananan yara fiye 2,300.
A cewar Abdullah Abu Shawesh, hare-haren sun kuma yi sanadin hallaka mata kusan 1,500.
Isra’ila dai ta lashi takobin wargaza kungiyar Hamas, wadda ta kai mummunan harin bazata, da ya yi sanadin kashe mutuwar mutum 1,400 tare da sace fiye da wasu 200.
Jakadan al’ummar Falasdinawan na wannan bayani ne yayin wani taron manema labarai da ya kira don sanar da duniya halin da ake ciki game da rikicin Isra’ila da Gaza da kuma yadda lamarin ya ranar Talata a Abuja, babban birnin Najeriya.
Abu Shawesh ya ce jimillar Falasdinawan da aka kashe tun daga ranar 7 ga watan Oktoba, sun kai 5791.
Jakadan ya kuma zargi kasashen Turai da mara baya ga Isra’ila kan abin da ya kira kisan kiyashin da take yi a yankunan Falasdin ba.
A cewarsa bai kamata a rika zaben dokokin kasashen duniya da za a yi aiki da su ba, sannan a yi watsi da wasu.
Abdullah Abu Shawesh ya ce matakin soja, bai taba yin aiki ba a lokutan baya, don haka ba zai yi aiki ba ma a wannan lokaci.


