An fara gudanar da zanga-zanga a biranen Ƙudus ta Tel Aviv a yau, yayin da mutanen a faɗin Isra’ila ke kiran gwamnatin ƙasar ta cimma yarjejeniya da ƙungiyar Hamas don gaggauta saki tare da maido da Isra’ilawan da ƙungiyar ke garkuwa da su a Gaza.
Nan hotunan wasu gungun jama’a ne da suka fara taruwa a wajen ofishin firaminista a Birinin Ƙudus.
Tun da farko Benjamin Netanyahu ya ce gwamnatinsa ba za ta ”saurara” ba har sai ta kama waɗanda suka kashe Isra’ilawa shidan da aka gano gawawakinsu ranar Asabar a Gaza.