Jagoran adawar Isra’ila, Yair Lapid ya yi kira ga mutanen ƙasar su fara ”babban yajin aiki” da maraicen yau, domin matsa wa gwamnati lamba to amince da yarjejeniyar tsagaita wuta don sakin Isra’ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
Tun da farko ƙungiyar iyalai da dangin mutanen da ake garkuwa da su, sun yi kiran gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar don neman firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu ya gaggauta ɗaukar mataki.
Mista Lapid ya yi kira ga kowane ɗan ƙasar da ya ce ”zuciyarsa ta sosu kan abin da ya faru” ya fito zanga-zangar, inda ya yi kira na musamman ga ma’aikata da hukumomi da manyan ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar da su ”dakatar da tattalin arzikin ƙasar”.
Kiran na zuwa ne bayan da a ranar Asabar, sojojin ƙasar suka gano gawar mutum shida daga cikin mutanen da ake garkuwa bayan sun mutu.