fidelitybank

Yahaya Bello ya karbi bakwancin taron Tijjaniyya a Kogi

Date:

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi a ranar Alhamis ya tarɓi Kalifan Tijjaniya Sheikh Ibrahim Niasse da kuma shugaban ƙungiyar a Najeriya Muhamnadu Sanusi yayin da ake gudanar da taron addu’o’i na neman zaman lafiya.

Kamfanin labarai na NAN ya rawaito yadda gwamnan ya tarɓi shugabannin tare da sauran malamai a taron da aka yi wa laƙabi da ‘hanyoyin rayuwa ta hanyar Sunnar Annabi’ da ke gudana a Lokoja babban birnin Kogi.

Taron wanda zai tara malamai daga ciki da wajen Najeriya, za a shafe kwana biyu daga 6 zuwa 8 ga watan Janairu ana gudanar da shi, inda za a gabatar da maƙaloli.

Za kuma a ziyarci marasa lafiya a asibitoci daban-daban tare da yin zikirin Juma’a da kuma liyafar cin abinci da sunan murnar samuwar Annabi Muhammadu – amincin Allah ya tabbata a gare shi.

Kazalika wani Khalifan na Tijjaniyya Sheikh Ali Arabi na halartar makamancin taron a Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Ganduje da Sarkin Kano Aminu Ado.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp