Diyar marigayi MKO Abiola, Hafsat Abiola-Costello, ta bayyana cewa, babu wani dan takara da ya fi cancanta ya jagoranci kuri’un matasa a Najeriya kamar Yahaya Bello.
Abiola-Costello wanda ita ce Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Yahaya Bello na 2023, ta bayyana haka a wata hira da aka yi da ita a ranar Talata a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na nan ya ruwaito.
Ta kara da cewa, a lokacin Yahaya a matsayin gwamnan jihar Kogi, kunɗin shiga na jihar ya karu daga Naira miliyan 350, zuwa Naira biliyan biyu.