Sugaban ƙasar Turkiyya kuma ɗan takarar jam’iyyar ‘People’s Alliance’, Recep Tayyip Erdoğan, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen shugaban ƙasar da ke gudana a faɗin ƙasar.
Shi ma babban abokin hamayyarsa ɗan takarar jam’iyyar ‘National Alliance’ Kemal Kılıçdaroğlu, ya kaɗa tasa ƙuri’ar a birnin Ankara.
Erdogan tare da matarsa Emine Erdoğan sun kaɗa tasu ƙuri’ar ne a gundumar Üsküdar da ke birnin Santanbul.
Bayan kaɗa ƙuri’ar tasa Mista Erdogan ya ce ya samu labari daga ministan cikin gida na ƙasar cewa zaɓen yana tafiya yadda ya kamata.
Kimanin masu zaɓe kusan miliyan 64 ne ake sa ran za su kaɗa ƙuri’unsu a zaɓen.