fidelitybank

Yadda za mu kashe Naira bilitan 3.5 wajen kwaso ‘yan Najeriya daga Ukraine

Date:

Ƙaramin Ministan Harkokin Waje a Najeriya Zubairu Dada ya yi ƙarin bayani game da kuɗin da za a kashe na dala miliyan takwas da rabi kwatankwacin Naira biliyan 3.5, wajen kwashe ‘yan ƙasar da yaƙi ya kora daga Ukraine.

Ya ce daga cikin ayyukan har da kula da waɗanda suka ƙi yarda su koma gida.

“Kar ku manta cewa aikin ya ƙunshi kula da ‘yan Najeriyar da babu mamaki ba za su yarda su dawo ba, da kuma sauran ayyukan ciyarwa da ofisoshin za su yi. Za mu yi sawu da yawa da ake buƙata” a cewarsa.

“Kuma su ma kansu ofisoshin suna cikin tsananin buƙata…hatta ofishin jakadancimu na Ukraine sai an ɗauke shi daga ƙasar.

“Saboda haka idan akwai wani ɗan Najeriya da aka bari a ƙasar, za mu ci gaba da yi masa addu’a kar wani abin ƙi ya same shi.”

Wani bidiyo da babban jami’in ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ya wallafa a shafinsa na Twitter ya nuna ‘yan ƙasar na ƙoƙarin hawa jirgin da gwamnati ta tura musu a Warsaw na Poland ranar Alhamis.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp