Hotunan tauraron dan adam sun nuna yadda aka yi kaca-kaca da wani sansanin sojin sama da ke yankin Crimea, wanda ya sha luguden bama-bamai a ranar Talata.
Wakilin BBC ya ce a kalla za a iya ganin jiragen yakin Rasha takwas wadanda aka lalata.
An kuma ga alamun ramukan da bama-bamai suka yi a inda suka fada, yayin da wuta ta ƙone wani makeken fili.
Ukraine ta nuna cewar ita ce ta yi wa Rashar wannan ɓarna ba tare da ta bayyana yadda ta kai harin ba, daga wurin mai nisan sama da kilomita 150 daga bakin daga.
Sai dai Rasha ta ɗora alhakin lamarin kan fashewar wani abu a wani wurin ajiye makamai, kuma ta musanta cewar an lalata wani wuri.


