A ranar Lahadi ne wata tankar man fetur ta fashe a garin Kontagora da ke jihar Neja, lamarin da ya jefa firgici a zukatan mutanen yankin da masu motoci.
Sai dai ba a samu rahoton wani ya mutu ba a fashewar, wadda ta auku a gidan man AA Rano da ke daura da babban asibitin Kontagora.
Wani ganau ya ce tankar ta kama da wuta, sannan baƙin hayaƙi ya turnuƙe, amma tankar ce kawai ta ƙone, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja, Hussaini Ibrahim, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce jami’an kashe gobara sun isa da sauri domin hana gobarar faɗaɗa, sannan ya ce babu wanda ya rasa ransa.


