Awannin da aka shafe ana ruwan sama a Abuja babban birnin Najeriya ya haddasa ambaliyar ruwa a wasu sassan birnin a safiyar yau Laraba.
Mazauna unguwar Lokogoma sun wayi gari cikin ruwa, inda ya hana ababen hawa sakat.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda ruwan ya kkusa shanye wata mota.
“Sai dai kawai mu yi addu’a, abin da ruwan safiyar nan ya haifar kenan, Lokogoma kenan,” in ji muryar waddda ta É—auki bidiyon.
An yi ta ruwa a Abuja tun daga asuba har zuwa misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Laraba.