Al’ummar musulmi a Jamhuriyar Nijar, sun yi idin Sallah bayan sanar da ganin watan Shawwal a ƙasar, abin da ya kawo ƙarshen azumin watan Ramadana a Nijar.
A daren Asabar al’umma ƙasar a ɓangrori daban-daban suka tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal abinda hukumar ƙolin ƙasar ta musulunci da ma gwamnati suka tabbatar bayan cikakken bincike.
Sai dai a wasu ƙasashe da dama ba a yi Sallah ba sai Litinin saboda rashin ganin watan na Sallah.