Rundunar ‘yan sanda a Bayelsa, ta ce wasu mutane sun banka wa wani barawon wayar salula wuta a Yenagoa, babban birnin jihar.
Rundunar ta ce mazauna unguwar da lamarin da ya afku sun fusata bayan da suka ga mutumin da ya kwaci wayar na kokarin gudu bayan ya kwaci wayar daga hannun wani mutum.
Lamarin dai ya afku ne a ranar Laraba.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, ya rawaito cewa, wasu mazauna unguwar na ganin matasan sun fara dukan mutumin da ya kwaci wayar sai suka kira ‘yan sanda to amma kafin zuwansu tuni suka banka masa wuta.
Da yake mayar da martani kan afkuwar lamarin, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya yi alawadai da kisan mutumin, sannan ya bayyana takaicinsa na rashin zuwan jami’ansu wajen a kan kari.
Jami’in dan sandan ya kuma gargadi mazauna birnin da su guji daukar doka da kansu.


