Masu masaukin baƙi a gasar Afcon ta 2023 Ivory Coast ta yi nasara kan abokiyar karawarta Guinea Bissau da ci biyu babu ko daya a wasan farko.
Seko Fofana ne ya ci wa ƙasarsa kwallo farko a minti na hudu da fara wasan, yanzu suna saman rukunin A kenan.
Jean-Philippe Krasso shi ne ya ci wa mai masaukin baƙi kwallo ta biyu bayan dawowa hutun rabin lokacin.
An ƙara wata shida kan lokacin da aka saba yin Afcon na 203 zuwa farkon 2024 – domin a kaucewa damin da ake fuskanta a yammacin Afrika, Amma jinkirin ya taimakawa Ivory Coast wajen kammala shirye-shiryenta, kuma za ta kashe dala biliyan daya wajen ɗaukar baƙuncin wasan.
Kasar da ke neman lashe gasar karo na uku bayan wadanda ta ci a 1992 da 2015, za su fara wasansu ne ba tare da babban ɗan wasan gabansu Sebastien Haller sakamakon rauni.
Wasannin ranar Lahadi sune
Rukunin A: Nigeria da Equatorial Guinea, a filin wasa na Alassane Ouattara da ke Abidjan (5pm ET)
Rukunin B: Egypt da Mozambique, A filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke Abidjan (2pm ET)
Rukunin B: Ghana da Cape Verde, A filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke Abidjan (5pm ET)