Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar hukumar Bokkos na jihar Filato, inda suka hallaka mutum biyu tare da ƙona gidaje da kuma coci-coci.
An kai harin ne da tsakar dare ɗauke da manyan makamai waɗanda suka zarta na ƙungiyar ƴan sintiri da ke yankin.
Shugaban ƙungiyar ci gaban al’ummar Bokkos, Farmasun Fudang ya bayyana mutane biyun da aka kashe ma’ikata ne a wani coci, inda ya ce an kuma ƙona gidaje da dama da kuma coci-coci, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Fudang ya ce maharan sun kuma lalata gonaki sannan suka yi awon gaba da shanu da tumakai da awakai da agwagi har ma da abincin da aka adana.
“Sun zo ne ta hanyar Ding’ak da Kopmur duk da cewa akwai shingen binciken jami’an tsaro a wajen. Sojoji sun yi harbi a iska sai dai ba su fafata da maharan ba,” kamar yadda Fudang ya yi zargi.
Shugaban al’ummar ta Bokkos ya ce harin na zuwa ne kwanaki biyu da kai irin makamancinsa a al’ummar Ndimar – Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma ta jihar da su kai musu ɗaukin gaggawa tare da ganin an hukunta waɗanda ke far musu.