fidelitybank

Yadda kwamitin Ganduje ya cusa kwarin gwiwa a APC – Buni

Date:

Shugaban kwamitin riko da tsare-tsare na babban taron jam’iyyar APC, kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce, ayyukan da kwamitin kula da tsare-tsare, ya sanyawa jam’iyyar kwarin gwiwa gabanin babban taronta na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 26 ga Maris.

Da yake karbar bayanin shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje tare da sauran mambobin kungiyar a daren Asabar, Buni ya bayyana cewa, kwamitin ya ja kunnen ‘ya’yan jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya da cewa babban taron ta a ranar da aka tsayar ya na nan.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar, wadda PlatinumPost ta samu ta rawaito cewa, Buni na tabbatar da cewa, jam’iyyar ta shirya babban taro wanda ya kira hadin gwiwar dukkan mambobin jam’iyyar.

Shugaban ya yabawa kwamatin da ya ce, suna gudanar da ayyukan da suka dace, wajen ganin an gudanar da babban taron jam’iyyar.

Buni ya ce, kwamitin shi ne na biyu a kan babban kwamitin tsare-tsare na taro bisa la’akari da muhimmancinsa, wanda ya sanar da nadin Gwamna Ganduje ya shugabance shi tare da wasu jiga-jigan mambobin da ke da tarihin nasarori a ayyukansu.

Ya kuma bukaci kwamitin da ya yi aiki tare da sauran kwamitoci musamman ofishin kula da harkokin gwamnati da ke Abuja, duba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su halarci taron.

Tun da farko, shugaban kwamitin kula da ka’idoji, Gwamna Ganduje, ya bayyana cewa, an kammala daukar matasa maza da mata aiki a matsayin jami’an yarjejeniya da basu horo a wani bangare na aikin kwamitin.

Ya ce kwamitin ya kuma dukufa wajen samar da wani shiri na abubuwan da suka faru,bdomin samun nasarar babban taron jam’iyyar.

Gwamna Ganduje ya kuma mika godiyarsa ga Buni tare da yin alkawarin yin aiki da sauran kananan kwamitoci, domin ganin an shirya babban taro cikin nasara.

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp