Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Jordan ta ce, jiragen yaƙin ƙasar sun gudanar da aikin jefa kayan abinci ta sama a Gaza tare a na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
Jiragen sun jefa tan 25 na abinci da sauran muhimman abubuwa a Gaza.
Jiragen Jordan biyu ƙirar C-130 da wani na Daular Larabawan ne suka gudanar da aikin a yankuna da dama na zirin, a cewar rahoton.
Gidan talabijin ɗin ya ce aikin na yau shi ne na 127 jimilla da Jordan ta gudanar tun bayan fara yaƙin a Gaza a watan Oktoban 2023.