Gobara ta kone wa wani bangare na shahararriyar kasuwar kayan masarufi ta Singa a jihar Kano.
Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar tun lokacin suna ta kokarin shawo kan lamarin tun faruwar ta.
Aminiya ta fahimci cewa, wurin da wutar ta kama wani bangare ne na kamfanin Mimza.
Wani ma’aikacin kamfanin, Muhammad Abdullahi, ya ce, ba a san musabbabin faruwar lamarin ba amma ana zargin wutar lantarki.
“Shi ne babban kantin sayar da kamfani, suna adana yawancin Chewing gum, kayan zaki, madara da sauran abubuwa. Ba za mu iya cewa abin da ya haddasa gobarar ba, watakila wutar lantarki. An kira ni da safiyar nan cewa gobara ta kama shagonmu, a haka na yi sauri na zo na ga abin da ke faruwa.
Ba zan iya kididdige asarar da aka yi ba, a gaskiya, za ta zama miliyoyi domin ko jiya sun yi lodin kayayyaki na miliyoyin.”