Gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin Abdullahi Umar Ganduje mai barin gado ta gabatar da rahoton miƙa mulki ga zaɓaɓɓen gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
A wani ɗan taƙaitaccen taro da aka yi a Fadar gwamnati, Ganduje wanda ya sami wakilcin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji ya nanata ƙudirinsa na tabbatar da miƙa mulki salin alin ba tare da matsala ba.
Ya buƙaci gwamnati mai jiran gado ta yi nazari kan rahoton sannan ta gabatar da tsokacinta.
A nasa jawabin, zaɓaɓɓen gwamnan na Kano da ya samu wakilcin shugaban kwamitin karɓar mulki na Jam’iyyar NNPP, Dr Abdullahi Baffa Bichi, ya bayyana cewa kwamitin zai bai wa gwamna mai jiran gado rahoto sannan zai sanar da tsokacinsa idan har akwai.
“A wannan lokacin, saura sa’a 105 a miƙa mulki a jihar Kano a don haka mun ƙudiri aniyar tabbatar da karɓar mulki cikin salama don ci gaban Kano da al’ummarta.”
Wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamna mai jiran gado na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce za su fitar da bayanai game da bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnati bayan cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati mai ci da mai barin gado.