fidelitybank

Yadda EFCC ta gano Naira biliyan 30 da Beta Edu ta wawushe

Date:

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta gano Naira biliyan 30 a wajen ministar ma’aikatar jin kai da aka dakatar, Betta Edu.

Haka kuma ta ce tana gudanar da bincike kan wasu asussan banki 50 duka a cikin badakalar kuɗaɗe da aka yi a ma’aikatar.

Shugaban hukumar ta EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana haka, inda ya ce akwai buƙatar a kafa kotuna na musamman waɗanda za su lura da shari’oin zargin cin hanci.

Olukoyode ya ce kuɗaɗen da aka kwato na cikin asusun gwamnatin tarayya a halin yanzu.

EFCC dai na gudanar da binciken badakalar da aka samu a ma’aikatar jin kai da ta shafi ministar da aka dakatar, Betta Edu, da tsohuwar ministar ma’aikatar, Sadiya Umar-Farouq, da kuma Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA.

A watan Janairu ne dai shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Edu sakamakon badakalar kuɗaɗe a ma’aikatar.

Daga nan ne EFCC ta kira ta domin amsa tambayoyi bayan fitar wata takarda da ta nuna cewa Betta ta ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa’idar aiki.

A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.

Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma’aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.

Betta Edu, ‘yar shekara 37, wadda ita ce matashiya mafi ƙaranci shekaru a jerin ministocin Tinubu, daga bisani ta ce ƙulle-ƙulle ne kawai ake yi don a ɓata mata suna, ta ƙara da cewa ba za ta yi almundahana da duniyar gwamnati ba

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp