Matatar mai ta Dangote ta ce, ta rage farashin litar man fetir zuwa naira 899.50 gabanin bikin kirsimati da sabuwar shekara.
Kakakin matatar Anthony Chiejina, ya ce an rage farashin litar man ne domin rage tsadar sufuri ga jama’a, a lokacin shagulgulan Ć™arshen shekara.
A cikin watan Nuwamba ma, matatar man mai zaman kanta ta rage farashin litar mai zuwa naira 970.
Ya ce “Domin samar da sauĆ™i kan sufuri a lokacin hutun Ć™arshen shekara, matatar mai ta Dangote ta fara sayar da mai a kan ragin farashi. Daga yau za a riĆ™a sayar da man a kan naira 899.50 a kowacce lita, daga mtatar man tamu.”
Chiejina ya jaddada cewa matatar ta jajirce wajen tabbatar da ganin an samarwa jama’ar Najeriya man fetir mai inganci kuma cikin farashi marar tsada.