fidelitybank

Yadda APC ta ɗauki Lauyoyi 12 don tunkara Atiku da Obi

Date:

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zaɓi manyan ƙwararrun lauyoyi 12, domin tsaya mata a shari’ar ƙorafin da jam’iyyun adawa za su shigar domin ƙalubalantar nasarar jam’iyar a zaɓen shugaban ƙasa.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta hannun babban mai bayar da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar Ahmad El-Marzuq, ya ce tawagar lauyoyin masana fannin shari’a ne, waɗanda kuma ya ce suke da ƙwarewa kan ƙararrakin zaɓe, sannan masu cikakkiyar masaniya game da kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa.

Ya ce tawagar manyan lauyoyin12 ƙarƙashin jagorancin fitaccen lauyan ƙasar Prince Lateef Fagbemi, za su kare nasarar da jam’iyyar ta samu a zaɓen a gaban kotu.

Manyan jam’iyyun adawar ƙasar na PDP da LP ne dai suka ce za su garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar cikin watan da ya gabata.

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A dawo da tallafin aikin Hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijawa kan harkokin ƙasashen waje...

A na fargabar mutuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari

Kamfanin dillancin labaru na AP ya rawaito cewa, shugaban...

An kwashe wasu daga cikin Gawarwakin da Jirgi ya fada cikin gidaje a Indiya

Ƙungiyar likitoci ta ƙasar Indiya (FAIMA), ta ce an...

Tinubu ya mayar da martani kan mayar da Najeriya tsarin jam’iyya daya

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mayar da martani game...

Zan cigaba da sa yawan jini ga maƙiya Tinubu – Wike

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin...

Tinubu zai magantu a kan ranar Dimokradiyya

Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi jawabi ga...

A shirye nake na mutu don nasarar APC a 2027 – Orji Kalu

Sanatan Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana...

Bayan hutun Sallah Tinubu zai koma Abuja

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu na kan hanyarsa ta komawa...

Mutane 570 aka kashe a Najeriya cikin watan Afrilu – Rahoto

Hukumar kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya ta ce, adadin...

PDP ba za ta mutu ba duk da rikicin cikin gida – Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ce...

Sojoji sun kashe riƙaƙen ɗan bindiga Guddel a Kaduna

Sojoji sun yi nasarar kawar da fitaccen shugaban ‘yan...

Fadar shugaban ƙasa ta yi kakkausar gargaɗi a kan Ndume

Fadar shugaban kasa ta yi kakkausar gargadi ga dan...
X whatsapp