Rahotonni daga birnin Yola na jihar Adamawa na cewa, ambaliyar ruwa ta mamaye wani ɓangare na garin da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce wuraren da ambaliyar ta fi shafa su ne Shagari Low cost, da Sabon Pegi, da Modire Yolde Pate da ke ƙaramar hukumar Yola ta Kudu.
Ya wallafa hotunan dakarun rundunar da suka ƙware a fannin koguna cikin jiragen ruwa da ke kan hanyarsu ta kai agaji ga al’ummomin yankunan.
A ɗaya daga cikin wuraren, zurfin ruwan ya kai rabin tsawon mutum.