A yanzu haka dai alumma na ta tururuwa domin zuwa ta’aziyya da kuma jana’izar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi 15 ga watan Yulin 2025 a birnin Landan.
Mutane da dama sun isa jihar tun a jiya Litinin, inda wasu ke Katsina domin tarbar gawar sa, yayin da wasu kuma suka wuce kai tsaye zuwa Daura inda za a yi janaizar marigayin.
Mutanen sun haÉ—a da wasu sannanu a Æ™asar ciki har da manyan Æ´an siyasa kamar tsohon gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, tsohon shugaban ma’aikata a fadar gwamnatin shugaba Buhari Farfesa Gambari da Arc Ahmed Musa Dangiwa, sai tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufai, da Sunday Dare, da mai magana da yawun Buhari Garba Shehu, sai Malam Isa Ali Pantami da kuma dai dai kun Æ´an Najeriya.
A yanzu haka gidan marigayin da kuma jihar na cike da jam’ian tsaro inda Æ´an sanda da jami’an tsaron farin kaya suka jibge É—aruruwan jam’iansu.
Rahotanni na cewa bayan an kawo mamacin, za a soma kai shi gidan sa da ke Daura domin yan uwa su yi masa adduoi, daga nan a kai shi fadar mai martaba sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk domin yi masa Sallah, daga bisani kuma a sake mayar da gawar gidansa domin birne sa.